A yau talata 13 ga watan Fabrairu ake bukin Ranar Rediyo ta Duniya, ranar da Hukumar Ilmi, Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, ta ware musamman domin karrama irin gudumawar da na'urar rediyo ta bayar ga ci gaban bil Adama a duk fadin duniya.
Wakilin Muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad, ya tattauna da masu harkar rediyo a Bauchi, cikinsu har da shugaban Kungiyar Masu Sauraron Gidajen Rediyon Gida da na Waje a Jihar Bauchi, Malam Sadisu Rabin Dami, wanda yace a yau talatar sun shirya karrama gidajen rediyon dake cikin Jihar tare da wakilan kafofin yada labarai na kasashen waje da na wasu sassan Najeriya dake aikawa da rahotanni daga Bauchi.
Yace sun gayyaci manyan sarakuna da sauran shugabanni na siyasa da kasuwanci da ma 'yan jarida zuwa taro na musamman da zasu yi.
Haka kuma yace zasu karrama wasu daga cikin 'ya'yansu da suka yi fice a wannan shekara wajen sauraron rediyo.
Sakataren kungiyar ta masu sauraren kafafen yada labarai a Jihar Bauchi, Mudassir Muhammad Tafawa Balewa, yace duk da irin barazanar da ta yi ta fuskanta, rediyo ta ci gaba da kasancewa mai matukar muhimmanci wajen sadarwa a tsakanin al'ummar duniya.
Yayi bayanin cewa na'urar rediyo ta kawo saukin sanin abinda duniya ke ciki a saboda cikin sauki da araha, mutum zai iya jin l;abaran abubuwan dake faruwa a ko ina a duniya.
Alhaji Sagir Madakin Shira yace talaka yana amfana sosai da rediyo, ya kuma jinjina ma gidan rediyon Muryar Amurka a saboda irin shirye-shiryenta na kwatowa da talakawa da marasa galihu hakkokinsu.
Facebook Forum