An samu jerin girgizar kasa da aman duwatsu daura da karshen yankin tekun Pacific a yau Talata.
Hukumar da ke bincike kan yanayin doron kasa ta Amurka ta ce, wata gagarumar girgizar kasa mai karfin maki 8.2 ta auku kilomita 280, kudu maso gabashin Tsibirin Kodiak da ke Alaska, lamarin da ya janyo aka sa jami’an ba da agajin gaggawa suka shiga shirin ko-ta-kwana, domin yin gargadi kan aukuwar bala’in Tsunami a yankin Alaska da British Columbia mallakar Canada,.
Sannan har ila yau, an saka daukacin gabar tekun yammacin Amurka da yankin Pacific da ke Hawaii a matakin shirin ko-ta-kwana domin gujewa bala’in na Tsunami.
Cikin gaggawa, an bai wa mazauna yankin shawarar su fice daga yankin su koma wurare masu tudu.
Daga baya, Cibiyar da ke aikewa da gargadin aukuwar Tsunami a yankin Pacific, ta soke wannan gargadi a yankin Hawaii.
Amma sauran yankunan da suka hada da gabar tekun Alaska da British Columbia da kuma wasu sassan gabar tekun yammacin Amurka, sun ci gaba da kasancewa cikin shirin shirin na ko-ta-kwana.
Facebook Forum