Taken wannan rana dai shine ‘a kawar da maleriya kwata-kwata a doron ‘kasa’ wanda ake batun cewa yana haddasa mutuwar ‘kananan yara da manya masu yawan gaske musamman ma a nahiyar Afirka.
Wata kididdiga da ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Borno ta fitar na nuni da cewa fiye da mutane Dubu 750 suka kamu da cutar zazzabin cizon sauro. Haka zalika ana samun kusan kashi 53 cikin 100 na ‘kananan yara da zazzabin cizon sauro ya halaka a jihar Borno cikin shekarar 2016.
Daraktan ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Borno, Mala A Waziri, yace cikin matakan da suke ‘dauka suna bayar da gidan sauro, haka kuma gwamnati na bayar da magunguna kyauta ga wadanda suka kamu da wannan cuta.
Ganin yadda ake samun yawaitar sauro ne sakamakon rashin kyan muhalli, hakan yasa wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda ya tambayi shugaban hukumar kula da muhalli ta jihar Borno, Alhaji Nasiru Ali Surundi, wanda yace yanzu haka suna yin feshi a mugudanan ruwa da bola domin kashe kwaya-kwayan sauro don rage yaduwar cutar.
Matsalar zazzabin cizon sauro na ‘daya daga cikin manya-manyan cututtuka da ke addabar al’umma musamman ‘kananan yara.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Facebook Forum