Musulmi a fadin Duniya suna sallar azumi da hutu na kwana uku domin kammala azumin watan Ramadan.
Hukumomin saudiyya sun bada labarin anga wata,sabo da haka jiya litinin ce rana ta karshe a azumin bana, kuma yau talata ce za a yi salla. Haka ma Masar da wasu kasashen larabawa da yawa sunce suma yau Talata zasuyi sallah.
Yau ce ranar farko na watan Shawwal, kuma rana ce ta babban hutu. Domin galibin muhimman lokutan ibadun Islama sun dogara kan ganin wata, sabo da haka lokacin yana iya banbanta cikin kasashe daban daban.