Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shan Miyagun Kwayoyi Ya Zama Ruwan Dare Gama Gari


Miyagun Kwayoyi
Miyagun Kwayoyi

Yanzu shan miyagun kwayoyi ya zama ruwan dare gama gari inda a kwanakin baya wani matshi a jihar Taraba yayi yunkurin kashe mahaifinsa kafin ya bankawa kansa wuta.

Kwanan nan a jihar Taraba wasu matasa suka kashe kawunansu bayan sun sha wasu muggan kwayoyi.

Shan muggan kwayoyi da wasu matasa keyi yana kara tadawa iyaye hankula musamman a jihar Taraba.

Sabili da magance matsalar shan muggan kwayoyi yasa wasu kungiyoyin sa kai da na addini suka yunkuro domin fadakar da matasa illar shan muggan kwaya.

Kungiyar matan Musulmai na cikin kungiyoyin da suka tashi haikan wajen fadakar da matasa da ceto wadanda suka fada cikin wannan bala'in. Kungiyar ta shiryawa matasan da suka tuba suka daina shan muggan kwayoyi taron bita wanda ya samu halartar masana da kuma tsoffin'yan jajaliya.

Dr. Sale Waziri daya daga cikin masanan da suka bada kasida yace samari da 'yan matan Najeriya tarbiyarsu ta gurbace. Sun lalace sai shaye-shaye duk da su ne shugabannin gobe. Dalili ke nan da suke kokarin cetosu kada gobe kasar ta zama bata da wasu mutanen kirki duk an taru an zama mashayan kwaya lalatattu.

Yanzu idan yara sun dawo daga makaranta babu wanda zai tambayesu abun da suka koya domin babu kowa. Iyaye sun tafi neman abun hannu. Dalili ke nan yara suka tashi da mugayen dabi'u. Duk gwamnatin da ta bar yara suna lalacewa bata san abun da ta keyi ba ke nan. Yakamata gwamnati ta tashi ta tarbiyantar da al'umma saboda a samu mutane nagari. Idan gwamnati ta bari yara suka tashi da mugayen halaye da wuya kasar ta zama daya.

Hajiya Zainab Ibrahim shugabar kungiyar Amirah a jihar Taraba tace a matsayinsu na iyaye mata idan damuwa ta taso cikin al'umma su ne suke daukan sakamakon da damuwar ta haifa, musamman idan ta shafi matasa. Matasa sun tasar ma lalacewa domin babu tarbiya yanzu lamarin da ya haddasa yawan shaye-shaye.

Wasu da suka tuba sun bayyana dalilin dake sa matasa shiga shan muggan kwayoyi. Rashin lissafi na daya daga cikin dalilan da yasa matasa suna shan kwaya.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG