Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ake Zaben Shugaban Kasa A Nijar


Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Salou Djibo.
Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Salou Djibo.

A yau litinin ake yin zaben shugaban kasa a jamahuriyar Nijer ta yammacin Afirka, hakan kuwa a wani kokarin neman maye gurbin mulkin soji da gwamnatin farar hula mai dorewa.

A yau litinin ake yin zaben shugaban kasa a jamahuriyar Nijer ta yammacin Afirka, hakan kuwa a wani kokarin neman maye gurbin mulkin soji da gwamnatin farar hula mai dorewa.

Akwai ‘yan takara goma, kuma wasun su, sun yi alaka ta kut da kut da shugaban da aka hambare Mamadou Tandja wanda ke gidan kaso yanzu haka bisa zargin shi da azurta kai ba a kan ka’ida ba.

A watan fabarairun da ya gabata sojoji su ka kawar da Mr.Tandja daga mulki lokacin da ya yi kokarin yiwa kundin tsarin mulkin kasa kwaskwarimar tsawaita mulkin shi bayan shekaru goma.

Shugabannin mulkin sojin kasar sun yi alkawarin maida kasar ga mulkin farar hula.

Jamahuriyar Nijer babbar mai arzikin ma’adinin uranium ce, amma duk da haka ta na fama da manyan matsalolin da suka hada da neman farfadowa daga tsananin rashin abinci, da rashin aikin yi, ga kuma barazanar al-Qaida daga arewacin Afirka.

Tun daga shekarar 1993 wannan ne karo na ukku da kasar jamahuriyar Nijer ke kokarin kafa gwamnatin farar hula bayan sojoji sun shafe wani lokaci su na mulki.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG