Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nicolas Sarkozy Ya Gargadi Shugabannin Afirka.


Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy.
Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy.

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya ja hankulan shugabannin kasashen Afirka da cewa su yi taka tsan-tsan, kuma su girmama abubuwan da al’ummomin su ke so ko kuma su fuskanci boren jama’a.

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya ja hankulan shugabannin kasashen Afirka da cewa su yi taka tsan-tsan, kuma su girmama abubuwan da al’ummomin su ke so ko kuma su fuskanci boren jama’a.

A jiya lahadi shugaban na kasar Faransa Mr.Sarkozy ya yi wannan furuci a Addis Ababa a wurin taron kolin da kungiyar kasashen Afirka ke yi a daidai lokacin da ake ci gaba da yiwa shugaba Hosni Mubarak zanga-zangar gama gari.

Shugaban na kasar Faransa yace al’ummar kowace kasa na bukatar shugabanci na gari, da demokradiya da kuma girmama hakkokin bil Adama. Ya ce ko dai shugabanni su yi kokarin canza abubuwa ko kuma guguwar canji ta yi gaba da su.

Haka kuma, Mr.Sarkozy ya bayyana goyon baya ga kokarin da kungiyar kasashen Afirka ke yi da nufin raba shugaban Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo da mulki. Kungiyar kasashen Afirka da MDD sun yarda da abokin jayayyar Mr. Gbagbo, Alassane Ouattara a matsayin mai nasara a zaben shugaban kasar da aka yi a cikin watan nuwamba.

Haka kuma a jiya lahadin shugaban Equatorial Guinea Tedoro Obiang Nguema Mbasogo ya karbi shugabancin kungiyar kasashen Afirka daga hannun shugaban kasar Malawi.

Amma kungiyar kare hakkokin bil Adama ta Human Rights Watch na kushewa sabon shugaban kungiyar, ta na mai bada hujjar cewa yadda Mr.Obiang ke tauye hakkokin bil Adama ya saba da manufar kungiyar kasashen Afirka ta bunkasa demokradiya da kyautata ta.

XS
SM
MD
LG