Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yara Milyan 5.9 Ne Ke Fama Da Matsalar Karancin Abinci A Najeriya - Majalisar Dinkin Duniya


Kayan abinci
Kayan abinci

Jami’in Majalisar Dinkin Duniyar ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da shirin Yaki da Karancin Abinci na bana.

Babban Jami’in Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da Ayukan Jin Kai a Najeriya, Muhammad Fall, ya bayyana cewar kimanin yara milyan 5 da dubu 900 ne ke fama da matsanancin karancin abinci mai gina jiki a Najeriya, adadi mafi yawa a fadin duniya.

Jami’in Majalisar Dinkin Duniyar ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da shirin Yaki da Karancin Abinci na bana.

A cewar Fall, manufar shirin ita ce daidaita zuba jari da ayyukan gwamnati a bangarorin bada tallafin abinci da kiwon lafiya da ruwan sha da tsaftar muhalli inda za’a fi maida hankali a jihohin arewa maso gabashin Najeriya da suka hada da Borno, Adamawa da Yobe.

Ya kara da cewar an samu rahoton cewar akwai yara dubu 700 ‘yan kasa da shekaru 5, dake fama da karancin abinci mai gina jiki a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

Fall ya cigaba da cewar ‘yan Najeriya miliyan 4 da dubu 800 na cikin hadarin fuskantar matsalar karancin cimaka a daminar bana (tsakanin watan Yuni da Satumba), wacce matsalolin ambaliyar ruwa da hauhawar farashin kayan masarufi da yakin Ukraine suka sake ta’azzara al’amura, abinda ya sanya samun abinci yayi matukar wahala.

Yace domin maida hankali akan mutane miliyan 2 da dubu 800 za’a bukaci Naira miliyan 306 domin gudanar da aikin a bana, da nufin kare sake tabarbarewar matsalar karancin cimaka a yankin zuwa wani al’amari mara dadi.

Hakan na zuwa ne bayan da najeriya ta ayyana dokar ta baci a fannin samun wadatar abinci a ranar 13 ga watan yulin 2023, sakamakon mummunan hauhawar farashin data kange dimbin al’umma daga iya sayen kayan masarufi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG