Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano: Hukumar Hisbah Ta Kama Matasa Maza Da Mata 20 Da Laifin Wanka Tare


Jami'an Hukumar Hisbah ta jihar Kano
Jami'an Hukumar Hisbah ta jihar Kano

Mataimakin kwamandan hukumar Hisbah Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar ya yi kira ga iyaye da su sa ido sosai kan harkokin ‘ya’yansu.

Hukumar ta Hisbah dake yaki da rashin da’a ta yi kamen ne a wani wurin shakatawa biyo bayan korafe-korafen da wasu mazauna yankin suka yi, a cewar kafafen yada labaran Najeriya.

Mataimakin kwamandan hukumar Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin.

Da yake karin haske kan yiwuwar sun aikata laifi, Dr. Abubakar ya ce wannan aika-aikar ta saba wa dokar Hisbah, wacce ta haramta wa maza da mata wanka tare.

Dr. Abubakar ya kara da cewa, da zarar aka kammala bincike za a hukunta wadanda ake zargi da aikata laifin. Ya kuma yi kira ga iyaye da su sa ido sosai kan harkar ‘ya’yansu.

Idan ba a manta ba, a baya-bayan nan, Hukumar ta gayyaci Murja Ibrahim Kunya, wadda ta yi suna a kafar Tik Tok, tare da wasu zuwa hedikwatar hukumar saboda ta yiwu suna bukatar gyaran hali.

Hakan dai na zuwa ne bayan da hukumar ta tsare Murja tare da wasu, saboda yin abubuwan da hukumar ta ce basu dace ba a shafukan sada zumunta a shekarar 2023.

A yanzu dai hukumar na bi a hankali wajen kawar da rashin da’a musamman a kafafen sada zumunta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG