Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Jam'iyyar Green Party Tayi Ikirarin Lashe Zaben Shugaban Kasar Amurka


Dr. Jill Stein, 'yar takarar shugaban kasar Amurka a karkashin Green Party
Dr. Jill Stein, 'yar takarar shugaban kasar Amurka a karkashin Green Party

Amurkawa jam'iyyu biyu kawai suka sani, wato Democrat da Republican, kuma da wuya su dubi jam'iyya ta ukku da idanun rahama saboda haka jam'iyyar Green Party ma bata yi tasiri ba a wannan zaben ba zai zama abun mamaki ba

Yayinda Hilary Clinton (ta jam’iyyar Democrats) da Donald Trump (na jam’iyyar Republicans) ke ci gaba da fafatawa a takaran shugaban kasa a zaben da za’ayi cikin watan Nuwamban wannan shekara a nan Amurka, wata ‘yar takara mai suna Jill Stein da ke takaran shugaban kasa a karkashin lemar jam’iyyar Green Party tace tana ganin duk ta fi damar lashe wannan zaben, duk da cewa galibi jam’iyyu biyu kawai aka fi sani a tsarin siyasar na Amurka – watau Democrat da Republican.

A wata cudanya da jama’a da tashar telebijin ta CNN ta shirya ne, Malama Stein ta fito tana bayyana Hilary Clinton a matsayin wadda “bata da natsuwa”, yayinda shi kuma Donald Trump tace “mutum ne dake cin mutuncin jinsunan mutane iri-iri da suka hada da baki ‘yan wasu kasashe, gashi da akidar nuna banbanci addini da launin fata, ga kuma surutun tsiya.”

A zaben shekarar 2000 an taba samun dan takaran shugaban kasa a wannan jam’iyyar ta Green party mai suna Ralph Nader wanda ya samu kashi 3 cikin 100 kawai na kuri’un da aka jefa, inda kuma karshenta George Bush na jam’iyyar Republican ya kada Al Gore na jam’iyyar Democrats.

Wasu na ganin shigar Nader a takaran ne ya baiwa Bush damar lashe zaben.

To amma ita Malama Stein tana ganin a wannan karon tana iya lashe zaben idan ta sami goyon bayan matasa miliyan 43 da take bi sau da kafa don samun goyon bayansu, musamman dalibbai da biyan bashin kudaden makaranta yayi musu katutu.

XS
SM
MD
LG