Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansandan Las Vegas Na Binciken Dalilin Kashe Mutane 59 tare da Jikata 500


'Yansanda suke wurin da aka yi harbi a Las Vegas
'Yansanda suke wurin da aka yi harbi a Las Vegas

‘Yan sanda a Las Vegas da ke jihar Nevada na laluben dalilin da ya sa wani mutum ya bude wuta akan taron jama’a da ke halartar wani wasan waka a daren ranar Lahadi, inda ya kashe akalla mutane 59, sannan ya jikkata wasu daruruwa, a harin da ba a taba ganin irinsa ba a Amurka a wannan zamanin.

‘Yan sandan Birnin na Las Vegas sun ce Stephen Paddock mai shekaru 64, wanda ya fito daga yankin Mesquite a jihar Nevada dake nan Amurka, ya kai harin ne a kan dandazon jama’ar da yawansu ya kai dubu 22, a wani budadden wuri da ake taron wasannin waka, inda ya yi ta cullo harsashai daga dakin otel dinsa dake bene na 32 a otel din da ake kira Mandalay Bay.

Hotel Mandalay Bay de Las Vegas inda harbin ya faru
Hotel Mandalay Bay de Las Vegas inda harbin ya faru

Shugaban ‘yan sandan Birnin na Las Vegas, Joseph Lombardo, ya ce nan da nan aka tura gwanayen ‘yan sandan na SWAT, wandanda suka burma dakin maharin inda suka tarar da shi a mace.

A cewar Lombardo, sun yi ammanar cewa Paddock ya kashe kansa ne, yayin da aka tsinci akalla bindigogi 10 a dakin otel din nasa.

Sai dai shugaban ‘yan sandan bai bayyana wannan hari a matsayin na ta’addanci ba.

“Da farko sai mun gano mene ne dalilinsa na kai wannan hari, sannan idan akwai wasu dalilai da ke da nasaba da ta’addanci baya ga cewa akwai yiwuwar mutum ne da ke cikin halin kuncin rayuwar da yake so ya halaka mutane da dama, lokaci ne zai ba mu dama, kafin mu saka wannan hari a cikin wannan aji.”

A jiya Litinin, shugaban Amurka Donald Trump, ya kwatanta harin a matsayin “tsantsan rashin imani”, sannan ya yabawa ‘yan sanda Birnin na Las Vegas kan yadda suka yi gaggawan kai dauki.

“Ina so na mika godiya ta ga ‘yan sandan Birnin Las Vegas da duk sauran wadanda suka kai daukin farko, saboda irin jarumtakar da suka nuna wajen ceto rayukan jama’a da dama. Abin al’ajabi idan aka yi la’akkari da irin zafin naman da suka nuna wajen dakile salwantar karin rayuka. Yadda aka gano maharin cikin gaggawa bayan harbin farko da ya yi, wani abu ne da za mu ci gaba da nuna godiya akai. Hakan ya nuna tsantsar kwarewa.”

A halin da ake ci, ‘yan sandan Las Vegas, na kokarin fahimtar dalilin da ya sa Stephen Paddock ya kai wannan hari, wanda shi ne mafi muni a tarihin Amurka a wannan zamani.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG