Yayin da ake bikin ranar mata ta duniya wato International Women's Day mai taken "An Equal World Is An Enabled World" wato Adalci na bai daya a duniya shine ke samar da adalci ga kowa.
Wata kungiya kare muradun mata a Najeriya mai suna “Aspire Women Forum” ta gudanar da taro, domin tattaunawa da mata da basu kwarin gwiwa game da yadda za su jajirce wajen taimakawa kansu da kuma bada gudunmawa a fannoni daban-daban na rayuwa.
Taron mai taken "Finding My Happy" wato gano abin da zai faranta min rai, ya samu halartar mata daga bangarori daban-daban, kuma ya mai da hankali ne wajen jan hankalin mata da su rika tallafawa juna tare da zama tsinstiya madaurinki daya.
Shugaban kungiyar Barista Zainab Marwa Abubakar ta ce dalilin taken shine 'yancin kowace mace ne ta kasance cikin farin ciki.
Wasu daga mahalarta taron sun ce irin wadannan tarukan nada matukar muhimmanci wajen ci gaban mata dama duniya baki daya.
Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar daga Abuja:
Facebook Forum