Shahararen kamfanin na me kirkiran kwamfutoci wato, Microsoft ya shiryar da wata horaswa ga kananan ‘yan kasuwa akan mahimanci amfani da runbun aje bayanai a Girgijen tafi da gidanka wanda ake kira Cluod a turance.
Don kara fahimtar wai menene wannan girgijen ko cloud da kuma amfanishi, kana da yadda yakamata ace matasa sun ci gajiyar amfani da shi, mun gayyato Bashir Gidado, Matawallen Achida, kadan da ga cikin bayanashi, ya bayyanar da wannan tsarin a matsayin girgije, wanda yake nuni da cewar mutane kan yi amfani da wannan girgijen wajen ajiye wasu sakonnin sirri nasu, da ma ajiye duk wani abu da zasu bukaci ajiyeshi har na tsawon wasu shekaru.
Kuma shi wannan tsarin ana iya amfani dashi a kowane irin na’ura matukar tana hade da yanar gizo. Kuma wannan matasa kan iya amfani da wannan girgijen wajen ajiye hotun, kasidu, rubuce-rubucen makaranta, hasalima mutun kan iya daukan darasi ta wannan tsarin wanda kana iya yin rubuce-rubucen, dalibi na iya aikawa da sako zuwa ga malamin shi a wata kasa, wanda kawai zai bukaci izinin ka ne kamin yasa mu ya shiga don duba wannan rubutun naka da kuma baka maki da yakamata, kuma dalibbi zai iya ganin abunda malaminshi yayi a wannan rubutun nashi.
Haka suma ‘yan kasuwa sukan iya amfani da wannan damar wajen tallata hajarsu, tunda wannan sashin na Girgije ana iya shiganshi kai tsaye a kowane lokaci aka so.
.