Mai horar da ‘yan wasan Arsenal Mikel Arteta ya ce ya zama wajibi ‘yan wasan kungiyar su koyi juriya akan ko wane irin yanayi suka sami kan su, bayan da suka nuna matukar bacin rai akan raunin da mai tsaron gida na kungiyar Bernd Leno, a wasan da Arsenal din ta sha kashi a hannun Brighton da da ci 2-1 a karshen mako.
A lokacin da ake ficewa da Leno a makarar maras lafiya sakamakon raunin, ya nuna yatsa wa dan wasan Brighton da suka yi karafkiya da shi Neal Maupay, lamarin da ya sa ‘yan wasan Arsenal din suka zagayen shi bayan kammala wasan kamar su dake shi, a yayin da wasu ma suka soma kaiwa ga jikinsa, kafin a shiga tsakani.
To sai dai Arteta na ganin ko da ‘yan wasa za su nuna bacin rai, to kamata yayi su yi shi a inda ya dace, kana kuma su fuskanci wasan da ke gabansu, kada su bari lamarin ya taba kuzarinsu.
An baiwa dan wasan baya David Luiz jan katin kora a wasan da Arsenal ta sha kashi a Hannun Manchester City a ranar Laraba, lamarin da ya sa ‘yan wasan na Arsenal shiga filin wasan Brighton da damuwa a zukatansu.
Facebook Forum