Wannan na zuwa ne a yayin da wasu suka yi batan dabo a wani lokacin da jama’ar kasar ke zaman makokin kisan wasu matasan gundumar Banibangou sama da 60 sakamakon arangamar da suka yi da ‘yan bindiga.
Bayanai daga ma’aikatar tsaron jamhuriyar Nijer sun ce wasu ‘yan ta’adda da suka zo, wasu a cikin motoci da dama, wasu kuma a kan gomman babura dauke da manyan makaman yaki sun yi yunkurin kai hari a kauyen Dangney na karkarar Anzourou. Sai dai sun ci karo da dakarun tsaron dake girke a kewayen garin inda aka shafe lokaci mai tsawo ana barin wuta.
Sakamakon farko na cewa sojan Nijer 11 sun rasu wasu 9 sun yi batan dabo yayin da 1 ya jikata, inji sanarwar hukumomin tsaro wacce ta kara da cewa babbar turjiyar da suka fuskanta daga askarawan gwamnatin Nijer ta tilastawa ‘yan ta’adda juyawa zuwa inda suka fito tare da kwashe gawawakin mutanensu.
Wannan al’amari na faruwa a wani lokacin da al’umar Nijer ke juyayin rasuwar wasu matasa kimanin 69 a wani dajin gundumar Banibangou abin da wasu ‘yan kasa ke cewa alamu ne dake nuna girman matsalar tsaron da ake fama da ita a jihar Tilabery.
Suna masu cewa ya zama wajibi shugaban kasa ya dauki kwararan matakai.
Shugaba Mohamed Bazoum wanda a farkon watan Satumba ya yi rangadi a karkarar Anzourou domin karfafawa jama’a gwiwa saboda tashin hankalin da suka yi fama da shi na shirin kai ziyara a gundumar Banibangou a karshen wannan mako domin jajantawa al’uma asarar rayukan gomman mutane da ‘yan ta’adda suka hallaka a ranar Talatar da ta gabata.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: