A karshen makon da ya gabata aka kama wani matashi a Kano dan shekara goma sha takwas zuwa ashirin mai suna Tanimu Ibrahim da zargin ya yiwa wata yarinya 'yar shekara hudu fyade.
Malam Garba Ibrahim shi ne mahaifin yarinyar da matashin ya yiwa fyade wanda kuma ya bayyana abun da ya faru kamar haka "Akwai wani da ya bude wani dan shago irin na galan galan yana sayarda dan su biskiti da alawas da dai sauransu sai ya kirata da ya kirata sai ya sa mata hannu a cikin pirijinta wanda ya kasance har ya ji mata ciwo ran Juma'a ke nan. Ban ankara ba sai washegari ranar Asabar wani makwafcina da motar hilux da mai honda muka cika a motoci muka dauki shi wannan accused person din muka runtuma zuwa Hisbah Board"
Daga hukumar Hisbah ta Kano sun je asibiti inda aka binciki yarinyar domin su tabbatar da abun da ya faru. Bayan binciken da ya nuna lallai an ji mata ciwo a pirijinta ne ita Hisbah ta mikawa 'yan sanda Tanimu Ibrahim wanda aka zarga da wannan muguwar aika aikar.
To sai dai Malam Garba Ibrahim yace a daidai lokacin da yake fama da bakin cikin lamarin da ya faru sai 'yan sanda suka ce lallai sai ya basu na goro wato cin hanci ke nan kafin su cigaba da maganar.
Bayan sun kai koke wurin 'yan sanda sai suka turasu ofishinsu dake kan France Road. A can ne aka fada masa cewa sai ya biya nera dubu daya kudin file wanda ya biya nan take. Bayan daukan bayyanansu Malam Garba Ibrahim ya ce sai 'yan sandan suk fada masa zai biya wasu kudade suka kuma nemi ya hada kai dasu. Sun fada masa "Akwai wasu dubu biyar wasu ma har dubu goma suke basu idan na bayar da wannan sai a kotu zan ga anfanin dubu biyar din"
Amma Malam Garba bai mallaki nera dubu biyar ba sai ya nemi a bari ya kawo washegari. Amma kafin gari ya waye sai ya sake tunani. Wanshekare da safe ya bugawa jami'in 'yan sandan waya ya ce "Na yi kokarin samun dubu biyar amma bata hadu ba. Idan na kawo dubu uku zaku karba" Jami'in yan sandan ya ce masa ya kawo kudin.
To sai dai wakilin Muryar Amurka Mahmud Kwari ya tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano ASP Musa Majiya dangane da batun wanda yace "Tuni har mai girma kwamishanan 'yan sanda bayan na sanarda shi ya bada umurnin duk wadanda suke wannan bagare musamman an gaya masa sunan wanda ake tuhuma a cikinsu yanzu na tabbatar maka kan cewa yana tsare kuma zamu tuntubi wanda aka ce ya bada cin hanci domin kara samun karfaffun hujjoji da kuma daukan matakin ladaftarwa...Da zara mun kammala bincikenmu zamu sanarda al'umma matakin da muka dauka a kan jami'an.