Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Hadaddiyar Masu Jigilar Shanu Daga Arewa Zuwa Kudu Tana Cigaba da Yajin Aiki


Kasuwar shanu
Kasuwar shanu

Sabanin yadda aka sanar a wasu kafofin yada labarai har da Muryar Amurka kungiyar masu jigilar shanu da wasu dabbobi daga arewacin Najeriya zuwa kudancin kasar sun musanta labarin

Hadaddiyar kungiyar masu jigilar shanu da sauran dabbobi daga arewacin Najeriya zuwa kudancin kasar sun musanta labarin da ake yayatawa cewa sun janye yajin aikin da suka fara.

Sakataren hadaddiyar kungiyar Abdullahi Adamu Shafir ya musanta labarin janye yajin aikin wanda wani ya yi ikirarin an yi hakan ranar goma ga wannan watan. Yayin da yake zantawa da Wakilin Muryar Amurka Abdullwahab Muhammed, sakataren yace " Akwai yajin aikin da muka shiga muke kiraye-kiraye mutanenmu har yanzu muna nan a cikin yajin aikin domin akwai wani wanda ya fito wanda ba mambanmu ba ne...yana cewa ya daidaita da gwamnati a janye yajin aiki har sai ranar 25 kafin nan za'a nemesu a kan tebur wanda mu ba'a yi haka da mu ba" Shi dai mutumin wai yayi bayani a gidan rediyon Faransa da Muryar Amurka.

Shi wannan bata garin wai yana wakiltar masu daukan kifi da albasa da dai makamanninsu. Sai dai ko suma da suke sana'a basu sanshi ba.

Malam Abdullahi yace suna nan kan bakansu. Ba zasu bar yajin aikin ba sai an biya masu bukatunsu. Yana kiran duk kungiyoyinsu su basu hadin kai domin su kwato wa kansu 'yanci. Yace abun da suke bukata musamman shi ne "A janye karban kudi a wurinmu a kan hanya ba bisa ka'ida ba"

Sakataren kungiyar reshen jihar Gombe Ali Sanata yace suna nan cikin yajin aikin, wato sun daina safarar shanu daga arewa zuwa kudancin Najeriya. Yace "Abun da muke bukata cutar da mu da a keyi in an zo da shanu daga arewa. In ka loda daga Gombe zaka tafi Fatakwal ko Legas sai ka kashe kudi nera dubu dari biyu da ashirin a kan hanya...Muna nema gwamnati ta waiwayemu a cikin yajin aikin. Muna nan."

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG