Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda Sun Kama Wata Mata Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Wani Yaro Dan Shekaru 3 Don Neman Kudin Fansa


Wata mata da ta yi garkuwa da karamin yaro
Wata mata da ta yi garkuwa da karamin yaro

A Najeriya yadda ake sako-sako da daukar matakan hukunta masu aikata laifukka na ci gaba da ingiza jama'a wajen aikata wadannan laifuka duk da hadarin da ke tattare da aikata su.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan kasar take rike da wata matar aure da take tuhuma da satar yaro dan shekara 3 don neman kudin fansa.

Batun satar mutane domin neman kudin fansa dai abu ne da ya jima yana sosa ran 'yan Najeriya, tare da kara jefa tsoro cikin zukatansu, musamman ganin yanzu ba matafiya kadai ba kowa na iya fadawa tarkon masu satar jama'ar.

Wata mata da ta yi garkuwa da karamin yaro
Wata mata da ta yi garkuwa da karamin yaro

Sau da yawa ana samun rahotannin kama masu wannan muguwar dabi'ar sai dai akasari daga nan ba za a kara jin komai ba, abinda wasu ke ganin shi ke kara bai wa masu dabi'ar damar ci gaba da ita har ma da shigowar wasu cikin aika aikar.

Rundunar 'yan sandan Najeriya yanzu haka tana rike da wata matar aure data kama a garin Gidan Madi na karamar hukumar Tangaza jihar Sakkwato da take tuhuma akan satar yaro dan shekara 3 dan makwabcinta don neman kudin fansa.

Kakakin Rundunar a Sakkwato ASP Sanusi Abubakar yace mahaifin yaron ne ya kawo karar cewa an sace dansa kuma an kira shi da wata Lambar waya ana neman ya biya naira miliyan 2 ko a kashe dansa, daga nan sai jami'an suka dukufa ga bincike.

Masu sharhi akan lamurran yau da kullum irinsu Farfesa Tukur Muhammad Baba, na ganin sakaci da ake nunawa wajen daukar matakan ladabtar da masu aikata laifuka na yin tasiri ga ci gaba da samun aikata laifukan.

Rundunar 'yan sandan dai ta ce idan ta kammala bincike akan wannan matar da ma wasu mutane da ta kama da aikata wasu laifuka za ta gabatar da su gaban kuliya, sai dai ‘yan Najeriya na fatan ganin ana hukunta masu irin wadannan laifuka ko zai kasance gargadi ga masu aikata makamantansu.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
XS
SM
MD
LG