Kungiyar da ta kunshi dalibai da wanda suka gama jami'a da dattawa da manyan ma'aikatan gwamnati har da ma wadanda suka yi ritaya , ta kuduri aniyar kwatowa yankin 'yanci. Kungiyar na neman gyara sha'anin tsaro da inganta noma, tattalin arziki da ilimi da gyara zamantakewar al'umma ba tare da la'akari da banbancin addini ko na kabilanci ba.
Ra'ayin masu kungiyar da suka fito daga duk jihohin arewa da birnin tarayya Abuja ya zo daya akan sabunta tarbiyar 'yan arewa da tunanensu a duk fannonin rayuwa kamar yadda aka san arewa a shekarun baya.
Tuni dai magabatan wannan gangamin farfado da kimar arewa da ma 'ya'yanta suka dukufa wajen fara shimfida gimshikin da zai sake sabuwar tafiyar lardin arewa kamar yadda Alhaji Abdulkarin Dayyabu ke fadi.
Ga karin bayani.