‘Yan Jam’iyyar Republican a Majalisar Wakilan Amurka, sun sauke Jim Jordan a matsayin dan takararsu a zaben cike gurbin kujerar Kakakin Majalisar.
Hakan dai na nufin an koma gidan jiya yayin da majalisar ta kwashe makonni babu tsayayyen shugaban da zai jagoran ce ta.
Matakin janye Jordan na jihar Ohio a takarar, na zuwa ne bayan da ya gaza samun adadin kuri’un da za su ba shi damar zama shugaban majalisar a lokacin da aka yi zaben a karo na uku.
Fusatattun ‘yan Republican sun nuna zakuwarsu na kawo karshen wannan takaddamar shugbanci tun bayan da suka tsige Kevin McCarthy.
Jordan ya kara fuskantar karin masu adawa da takararsa a zaben duk da cewa ya samu goyon baya daga tsohon shugaban Amurka Donald Trump.
‘Yan Republican sama da dozin biyu ne suka yi kememe suka ki zaben Jordan.
“Akwai bukatar mu hada kanmu, mu manta waye zai zama kakakin majalisar, zan yi aiki tukuru don taimakawa kowane ne saboda mu taimakawa Amurkawa.” In ji Jordan.
A ranar Litinin mai zuwa ‘yan Republican a Majalisar za su yi wani taro na musamman don fitar da tankarar da zai nemi maye gurbin Jordan.
Su dai dukkan ‘yan Democrat dan jam’iyyarsu Hakeem Jefferies suka zaba.
Dandalin Mu Tattauna