Akwai alamun ‘yan rajin kare demokradiyya za su yi nasara da gagarumin rinjaye, a zaben gundumomi da ya sami halartar dimbin jama’a, wanda ke nuna kin jinin gwamnatin Yankin Hong Kong.
Sakamakon farko da aka fitar da safiyar yau Litinin, ya nuna ‘yan takarar ‘yan rajin demokradiyya ne ke samun nasara a kusan dukkan kujerun da suke takara a majalisun gundumomi 18 na Hong Kong.
‘Yan rajin na kan gaba da kujeru 278 akan abokan hamayyar su da ke da kujeru 42.
Idan aka dore da hakan ko, zai kasance wani babban koma baya ga magoya bayan China, da suka mamaye kusan dukkan mukaman siyasa a Hong Kong.
Wannan kuma na zaman shaida ga ci gaba da samun goyon baya da ‘yan demokaradiyyar da aka kafa watanni 5 da suka gabata ke samu, wanda ke kara habaka kamar gobarar daji.
Zaben ba zai kawo wani gagarumin sauyi a tsarin siyasar Hong Kong ba. ‘Yan majalisar gundumomi ba su da karfin ikon kafa dokoki, suna dai kula ne mafi akasari, da lamurran da suka shafi gundumomi kamar korafin daga murya ko wuraren tashoshin motocin safa.
To sai dai ana daukan zaben na majalisun gundumomi a matsayin daya daga cikin manyan ma’aunan auna ra’ayin al’umma, kasancewar sa shine kadai zaben demokradiyya da ake yi a Hong Kong.
Kimanin mutane miliyan 3 ne suka jefa kuri’a a zaben wanda shine mafi samun halartar jama’a,
ya kuma ninka yawan jama’a a zaben da ya gabace shi a shekara ta 2015.
Facebook Forum