ABUJA, NIGERIA - A halin da ake ciki a Najeriya, kudin masara da buhun shinkafa na neman ninka albashin karamin ma’aikaci da masu karamin karfi.
Haka kuma hauhawar farashin kayan ya sa kananan yan kasuwa cikin fargaba da zulumi ta yadda mutane za su iya mallakar kayan abun sayarwa a kasuwa.
Hakan yasa ‘yan kasuwa musamman masu karamin jari, jarin nasu yake karyewa sakamakon tashin kaya a wurin sari da yawan karban bashi daga wurin masu sayan kaya.
A kasuwar Kaura dake babbin birnin tarayya Abuja mun ji yadda farashin kayan suke, inda ‘yan kasuwa suka bayyana yadda farashin kayan yake hawa da kuma dalilai.
Wani magidanci mai suna Ibrahim Muhammad ya ce halin da ake ciki na tsadar rayuwa kan kawo sabanin tsakanin iyali.
Auwal Kabir Indabawa, shi kuwa ya dora alhakin halin da ‘yan Najeriya ke ciki na tsananin rayuwa akan gwamnatin kasar.
Duk da haka ‘yan Najeriyar dai na ganin za a iya samun saukin rayuwa idan har gwamnati ta tsaya tsayin daka wajen yin abin da ya da ce, yayin da wasu ke ganin gazawar gwamnatin kasar wajen dogaro da man fetur, alhalin kasar tana da arzikin ma’adanai da na noma.
Saurari cikakken rahoto daga Hauwa Umar:
Dandalin Mu Tattauna