Sama da kashi 91 cikin 100 na masu kada kuri'a ne suka amince da sabon kundin tsarin mulkin, a zaben raba gardama da aka gudanar a ranar Asabar, in ji ministan harkokin cikin gida na Gabon Hermann Immongault a wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar.
Ya kara da cewa an kiyasta kashi masu kada kuri’a kashi 53.5 cikin 100 ne suka kada kuri’ar raba gardamar.
Kudurin daftarin tsarin mulkin, wanda ya nemi sauye-sauye masu yawa da za su iya hana mulkin gado na iyali daya da kuma mika mulki, sama da kashi 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada ake bukata kafin a amince da shi.
A shekarar 2023 ne sojoji suka hambarar da shugaba Ali Bongo Ondimba tare da yi ma shi daurin talala, inda suka zarge shi da yin rashin gaskiya da almubazzaranci wanda ya jefa kasar cikin rudani. Bayan mako guda gwamnatin mulkin sojan ta saki Ondimba bisa dalilan jinkai, inda ta ba shi damar zuwa kasar waje neman lafiya.
Sojojin sun ayyana babban hafsan tsaron kasar, Janar Brice Clotaire Oligui Nguema, a matsayin shugaban kwamitin rikon kwarya da zai jagoranci kasar. Oligui dan uwan Bongo ne.
Bongo ya yi wa'adi biyu tun bayan hawansa mulki a shekara ta 2009 bayan rasuwar mahaifinsa wanda ya shafe shekaru 41 yana mulkin kasar. ‘Yan kasar da yawa sun bayyana rashin gamsuwa da mulkinsa. Wani yunkurin juyin mulki da aka yi a kasar a shekarar 2019 ya ci tura.
Dandalin Mu Tattauna