Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasar Afrika Ta Kudu Suna Kada Kuri'u A Yau Laraba


A yau ake kada kuri'u a kasar Afrika ta Kudu, wanda zai bayyanar da makomar siyasar kasar.

Wannan Zaben gwaji ne ga jam'iyyar Shugaban kasa Cyril Ramaphosa, wato jam'iyyar ANC, wadda a baya ta yi matukar farin jini, ita ke mulki a kasar ta Afirka Ta Kudu tun daga lokacin da akidar wariyar launin fata ta zo karshe shekaru 25 da su ka gabata.

Mutuncin jam'iyyar ya zube saboda rashin ayyukan yi wanda ya kai matakin kashi 27% cikin dari, da kuma tabargazar almundahana wadda ta tilasta ma mutumin da Ramaphosa ya gada wato Jacob Zuma, daga ofishin a shekarar bara.

Ana kyautata zaton Jam'iyyar barden yaki da wariyar launin fata kuma ta tsohon Shugaban kasar Nelson Mandela, ita ce za ta ci zaben na yau Laraba, to amma ta na fuskantar babban kalubale daga babbar jam'iyyar adawa ta DA mai tsaka-tsakin ra'ayi da jam'iyyar EFF mai tsattsauran ra'ayin 'yan gaba dai gaba dai.

Ana sa ran za a sanar da sakamakon karshe a ranar Asabar mai zuwa, Jam'iyyar da ta yi rinjaye a majalisar dokokin Afrika ta Kudu, ita za ta zabi shugaban kasa, wanda za a rantsar da shi a ran 25 ga watan Mayu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG