Julius Berka dan shekaru talatin da biyu yana cikin wadanda suka yi jerin gwano a Yaounde jiya Litinin ana neman gwamnati ta bayyana inda aka kai fusunonin da suka bace.
Yace abin da muke bukata kawai shine gwamnati ta gaya mana inda suke. Bamu da wani mugun nufi. Muna da ‘yancin sanin inda suke.
An sauyawa fursunonin wurin zama ne bayan bore da aka yi a gidan yarin dake Kodengui ranar ishirin da biyu ga watan Yuli. ‘Yan awaren yankin Kamaru da ake amfani da harshen turancin Ingilishi da ke tsare a gidan yarin, da ‘yan hamayya, sun kwace ikon gidan yarin domin nuna fushinsa kan irin cunkoso da rashin kyaun muhallin gidan yarin da kuma tsawon lokacin da ake dauka kafin a gabatar da wadanda aka kulle gaban kotu.
Sama da mutane dubu shida ke kulle a gidan yarin da aka gina domin tsare mutane dari bakwai da hamsin.
Gwamnati tace, an sakewa kimanin fursunoni dari biyu da hamsin wuri bayan boren. ‘yan tawaye sun bada sanarwar ta hanyar sadarwar internet inda suka ba gwamnati wa’adin kwana biyar daga Laraba da ta gabata, ta gaya masu inda mutanen da aka tsare suke idan ba haka ba ta kuka da kanta.
Jiya litinin suka ce an gaya masu cewa mutane tamanin da takwas daga yankin da ake amfani da turancin ingilishi da ake tsare da su suna tsare a wani gidan yari dake birnin Yaounde. Suka ce basu san inda sauran mutanen da ake tsare da su suke ba.
Facebook Forum