Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyyar Nijar Ta Cika Shekaru 59 Da Samun 'Yancin Kai


Yau 3 ga watan Agusta, Jamhuriyyar Nijar take bikin cika shekaru 59 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

Albarakcin zagayowar wannan rana, shugaban kasar Issouhou Mahamadou, ya yi jawabi ga al’ummar kasar, inda ya tabo wasu muhimman batutuwa.

Matsalar tsaron da ta addabin yankin Sahel da ma Afirka ta yamma, su ne batutuwan da ke kan gaba a jawabin shugaba Issouhou na Nijar, kasar da turawan mulkin Faransa suka raina.

A cewar shi, matsalar ta tsaro ta kai ga shallin da kasashen duniya za su karkatar da hankalinsu, saboda haka kasar Nijar za ta ci gaba da gwagwarmaya domin ganar da mambobin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya cewa akwai bukatar tallafawa kasashen Sahel a yaki da ta’addanci.

Ya kara da cewa, Nijar za ta ci gaba da jan hankula don ganin an bai wa rikicin Libya kulawar da ta dace, a ci gaba da neman hanyoyin murkushe tashin hankali da ake fama da shi a yankin tafkin Chad da yakin Sahel.

Fannin diflomasiya na daga cikin fannonin da shugaba Issouhou ya ce, Jamhuriyar Nijar ta samu ci gaba sosai a ‘yan shekarun nan, misalin taron kungiyar tarayyar Afirka ta AU da ya gudana a watan jiya a birnin Yamai da shigarta sahun mambobin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, da kungiyar ECOWAS ke karkashin shugabancin Nijar, alamu ne da ke nunin kasar ta samu karbuwa a idon duniya.

Sai dai jami’in fafutuka Abdou Elhadji Idi na kungiyar FSCN na cewa ‘yancin kan Nijar wani abu ne da ke rubuce a takardar amma babu shi a zahiri.

Bunkasa ayyukan noma domin kawar da yunwa kafin shekarar 2021, da shirin bunkasa noma don samar da wadatar shinkafar cikin gida kafin 2023, na daga cikin ayyukan da shugaban kasar Nijar ya ce zai maida hankali akan su.

A yau 3 ga watan Agusta shugaban ya jagoranci bikin dasa itace a jihar Tahoua, kamar yadda a sauran jihohi ake gudanar da ayyukan dashen itace da nufin yaki da kwararowar hamada.

Ga cikakken rahoton Wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG