Shugaban hukumar zabe ko INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya jagoranci jami’ansa a gaban kwamitocin kula da harkar zabe na majalisar dattawan dana wakilai domin yin bayani dangane da kudin da suke nema na gudanar da zaben shekarar 2019.
Farfesa Mahmud Yakubu yace suna bukatar kudi kimanin Naira biliyan 189 ne da za su kasa gida hudu. A ciki za’a biya ma’aikata zabe da kwamgilar buga takardun zabe da bangaren gudanar da ayyukan zabe, sai kuma kudin da za’a ware domin bukatu na musamman.
Shugaban hukumar zaben y ace idan an yi la’akari da zaben shekarar 2015, Naira biliyan 120 ne kawai aka kashe. Amma yanzu hukumar na neman Naira biliyan 189, an samu karin Naira biliyan 69. Yace dalilin banbancin shi ne karin masu jefa kuri’a da aka samu. A shekarar 2015 mutane miliyan 70 ne aka yiwa rajista. Amma a wannan shekarar an samu karin mutane miliyan 12 da ‘yan kai. Idan aka kwatanta da na shekarar 2015 an samu mutane miliyan 82 da za su kada kuri’a a zaben 2019.
Sanata Suleiman Nazir shugaban kwamitin harkar zabe na majalisar dattawa yace zaman kwamiti daban yake. Idan sun gama abun da su keyi sai su kai gaban majalisun, ayi muhawara a kai.
Dangane da naurar nan mai tantance masu zabe, da ake cewa card reader da turance, Sanata Suleiman Nazir y ace naurar ce ta basu nasara a zaben 2015, saboda haka suka yi doka cewa ba za’a yi zabe a kasar ba sai da naurar. Naurar ta na hana yin magudi.
A saurari rahoton Medina Dauda
Facebook Forum