'Yan ta’addar Boko Haram na bullowa da sabbin hanyoyin yin barazana na iya kai hari manyan garuruwa, bayan sun yi kwantar bauna na wani lokaci.
Damuwar da sashen jinkai na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna kan yadda ‘yan Boko Haram kan sace ‘yan agaji, suna kashe su dama kai farmaki kan tawagarsu, ya kawo zullumi sosai musamman ma bayan yunkurin hari da ‘yan ta’addar su ka yi a Damaturu na jihar Yobe, inda jami’an tsaro su ka samu nasarar kwantar da fitinar.
Wannan ya zo ne kwanaki kadan bayan babban sufeton ‘yan sanda Muhammad Adamu ya ce da taimakon jama’a an samu nasarar kwance damarar wasu daga ‘yan ta’addar.
Wani mai rajin kare al’ummar Arewacin Najeriya mai suna Anas Dan Nayaba ya ce sai an samu garambawul ga lamarin jami’an tsaron kafin a cimma nasarar da a ke fata.
Bayan ya dawo daga wani rangadi don tabbatar da tsaro, gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya ce matakan da a ke daukawa na tasiri wajen wanzar da salama.
Tun a 2009 da Boko Haram ta bayyana a fili da kuma shiga zubar da jini, bana shekaru 10 kenan da a ke ta kuka da share hawaye don da alamu fitinar na neman zama jiki da kan sa jama’a yaki da tsoro.
Ga rahoto cikin sauti.
Facebook Forum