Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Rundunar 'Yan Sanda Guda Uku


Hotunan Mukadashin Sufeton Yan Sanda da Kwamandan Runudnar Tsaro Ta musamman A Maiduguri
Hotunan Mukadashin Sufeton Yan Sanda da Kwamandan Runudnar Tsaro Ta musamman A Maiduguri

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da mutuwar jami’anta uku, da wasu mutane biyu a kwanton bauna, da wasu ‘yan bindiga suka kai kan matafiya a hanyar Lafiya zuwa Akwanga dake jahar Nasarawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan na jihar Nasarawa, Isma’il Usman, a hirar su da wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji, yace yanzu dai komai ya lafa, kuma an tura jami’an tsaro don kare lafiyar al’umma a hanyar.

Wani dake aikin sufuri a kan hanyar da Muryar Amurka ta yi hira da shi yace a duk lokacin da direbobi zasu bi wannan hanya, fargaba suke, saboda, da rana ake tare hanyar ake fashi.

Ga cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG