Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan bindiga sun fille Kan wani Dan Majalisar Dokokin Jihar Anambra


'Yan Bindiga
'Yan Bindiga

Yan bindiga sun fille Kan wani Dan majalisar dokokin jihar Anambra Mai Suna Hon Dr. Ikechukwu Okoye bayan an sace shi a makon jiya

Rundunar Yan sandan jihar ta ce tana gudanar da wani sintiri na hadin gwiwa don ganin an kamo tare da hukunta wadanda suka kashe wannan dan majalisa.

Bayanai na numi da cewa, an tsinci kan dan majalisar da aka fille a gefen titi tare da wata wasika a mazabarsa da ke jihar ta Anambra.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ta kuma ce ta yi damara domin ganin cewa an gano an kuma hukumta wadanda suka kashe dan majalisar.

A hirar shi da Muryar Amurka, m ai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, DSP Akanga Anthony ya bayyana cewa, rundunar ‘yan sandan jihar tana gudanar da wani sintiri na hadin guiwa tare da sauran jami’an tsaro da ke sassa dabam daban na jihar.

Tuni gwamnatin jihar ta fitar da sanarwar inda ta bayyaka takaicin wannan lamari.

Saurari cikaken rahoton Lamido Abubakar sokoto cikin sauti:

Yan bindiga sun fille Kan wani Dan Majalisar Dokokin Jihar Anambra-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG