Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga da Ake Zaton yan Kungiyar Boko Haram ne Sun Kashe Mutane Ashirin da Biyar


Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.
Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Oktocba 2, 2014.

Wasu wadanda ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutane ashirin da biyar a garin Doron Baga, a arewa maso gabashin Nigeria.

Shedun gani da ido da hukumomi sunce wasu yan bindiga da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutane ashirin da biyar a garin Doron Baga, jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria.

Sun baiyana cewa yawancin wadanda aka kashe yan su ne a gari na Doron Baga dake lungu. Wasu shedun gani da ido ma sunce mutane arba'in ne aka kashe

A makon jiya, harin da ake zaton yan kungiyar Boko Haram ne suka kai ya kashe akalla mutane arba'i da biyar. Rahotanin sun baiyana cewa yan yakin sa kan sun kutsa kauyen Azaya Kura a yankin Mafa a ranar Laraba, suka kaiwa mazauna kauyen hari, suka lalata gidaje. Haka kuma yan yakin sa kan sun sace kayayyakin abinci da kaji.

Yawancin mazauna Mafa a karamar hukumar Mafa, kusan watani biyu da suka shige, suka arce daga gidajensu, bayan yan Boko Haram sun kafa ikonsu a yankin.

An dorawa yan kungiyar Boko Haram alhakin rasa dubban rayuka cikin shekaru biyar. Kungiyar ta kwace garuruwa da yan dama a jihohin Borno da Adamawa, wuraren data kira daular Islamiya.

XS
SM
MD
LG