Kungiyar ta kira 'yan Najeriya su shirya matuka su kare kansu domin komi ya bayyana a fili cewa jami'an tsaron kasar sun gaza wajen kare 'yan kasa.
Da yake jawabi a wurin taron manema labarai a garin Kaduna sakataren kungiyar na kasa Dr Khali Abubakar Aliyu yace duk da yake kungiyar ba tace a tada hankali ba amma bata yiwuwa mutum na tsaye a zo a hallakashi ba tare da yin wani abu ba.
Yace sun gaji da yadda ake zubar da jinisu. Sun gaji da lalata dukiyar al'ummarsu. Sun gaji da kashe samarinsu da ma shugabannin dake gabansu. Sun gaji da yadda ake yi masu barazana a inda suke zaune. Sun gaji da romon baka.
Akwai bangaren dokokin kasar da suka amincewa kowane dan kasa ya kare 'yancin kansa da ransa da dukiyoyinsa idan hukuma ta gagara yin hakan. Sabili da haka idan hukuma ta gagara ne to ta fito tayi bayani.
Suna kiran kowa cikin al'umma kada ya bari a zo ayi masa kaca-kaca kamar yadda aka saba gani yana faruwa. Bai kamata mutum ya bar kansa a zo a yankashi kamar an yanka kare ko akuya ba.
Duk da kiran 'yan kasa su kare kansu Dr Khali Aliyu ya kira da a dukufa da yin addu'a. Duka masallatai su tashi su yi addu'a ta musamman.
Ga karin bayani.