Duk wanda ya halarci jana'izar ya nuna bacin rai a fili saboda yanayin da dalibin Mala Bagale ya hadu da ajalinsa.
Sakatare janar na kungiyar daliban kasar Nijar Useni Sambo yace 'yan makarantar Nijar gaba daya dake cikin jihar Yamai da duk jama'ar kasar suna cikin takaici da bakin ciki da kunci saboda sun kawo dan uwansu wurin kwanciyarshi na karshe.
Injishi gobe zasu kai wasikar shirin yin jerin gwano cikin makonni masu zuwa saboda su gayawa Shugaban kasa ya kai ta'aziyarsa zuwa ga iyayen Mala Bagale.
Jin takaicin abun da ya samu dalibin sanadiyar samamen da 'yansanda suka kai Jami'ar Abdulmummuni da sunan murkushe zanga zanga ya sa shugabannin kungiyar dalibai ficewa daga zauren taron sulhu da wakilan gwamnati a karkashin Firayim Minista Birje Rafini da sa idon shugabannin addinai da na hukumar kare hakkin dan'Adam jiya da dare.
Bayan sun fito daga dakin taron Nasiru Munkaila na kungiyar dalibai yace manyan jami'an gwamnati da suka bada umurnin a kai samame a Jami'ar suna bukatan a fitar dasu daga mukamansu saboda a cewarsa sun yiwa kasar aikin asha. Yace kawo irin wadannan mutanen a ce su tattauna dasu suna ganin ba'a yi masu adalci ba, ba'a kuma girmama dalibin da aka kashe ba.
Firayim Ministan Nijar Birje Rafini na ganin ficewar shugabannin daliban ba zai hana fahimtar juna ba nan gaba. Yace sai a hankali, ana yi sannu sannu kafin a daidaita.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Facebook Forum