Kerry yace, babu abinda ya canza a sakamakon kulla yarjejeniyar da Amurka da sauran manyan kasashen duniya biyar sukayi da kasar Iraqi don dakatar da shirin ta na nukiliya. Inda aka amince da janye wasu takunkumi da aka kafa mata na biliyoyin daloli.
Ganawar, wacce aka yi a birnin Riyadh na Saudiyya, ta zo ne bayan wasu manyan al'amura masu nasaba da Iran, ciki har da aiwatar da yarjajjeniyar nukiliya, da kama wasu Amurkawa a jirgin ruwa na wani dan lokaci, da musayar fursunonin da ta kai ga sakin Amurkawa 4 da ke kurkuku a Iran, inda aka saki ba-Amurke na biyar a makon jiya.
Duk kuwa da faruwar wadannan al'amuran, Ministan Harkokin Wajen Saudiyya ya ce, "Ba na tsammanin huldar kud-da-kud ta na iya yiwuwa tsakanin Amurka da Iran.
Jubeir ya yi wannan kalamin ne yayin da shi da Kerry ke zaune kafada-da-kafada jiya Asabar a wani wurin taron manema labarai.