Directan kungiyar dake lura da kawar da kanjamau a jihar Plato (PLACA) Dr Francis Magaji, wanda ya baiyyana wannan ga manema labaru a Jos, yace manufar yin hakan shine domin a tanadas da yanayi nagari ga mutunen dake rayuwa da wannan cutar domin su sami kulawa mai kyau.
Dr Magaji, wanda ya marabci manema labaru a matsayin shirinsu na bukin ranar Kanjamau ta duniya, yace shirin dokar kauda kiyayya da ‘yan Majalisar jihar suka sawa hannu, zata karfafa mutane domin yin gwajin sanin matsayinsu, kare wadanda ke rayuwa da wannan kwayar cutar, tanada musu damar samun magani da kuma taimaka masu yin rayuwa kamar sauran mutane.
Yace "Akwai manufofi da yawa da gwamna Jonah Jang yake kokarin sa musu hannu domin aiki. Tuni an rigaya an fitar da kwafi na shirin dokar kawar da kiyayya da kuma nuna bambamci wadda ‘yan majalisa suka sawa hannu kuma kamin karshen shekara, za’a maida ita doka.”
Magaji ya kara da cewa idan ba’a kawar da kiyayya ba, mutane zasu ci gaba da mutuwa, domin ba zasu fitar da kansu don gwaji da magani ba.
Ya kuma ce "Ba wanda zai so ya fadi cewa yana da wannan cutas domin bayason kiyayyar mutane. Ba wanda kuma zai so a nuna masa bambanci. Idan aka tanada dokoki nagari, zai ba mutane damar fitowa su baiyyana matsayinsu kuma su sami tallafi.”