A cikin hirarshi da Sashen Hausa, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dake neman wa’adin mulki na biyu karkashin tutar Jam’iya mai mulki APC ya bayyana cewa, akwai banbancin tsakanin yadda ake samun wutar lantarki yanzu da yadda take shekaru hudu da suka wuce. Yace masu yin sana’oi suna shaida ci gaban da aka samu a wannan fannin wadanda a da suke amfani da janareta domin gudanar da sana’oinsu.
Shugaba Muhammadu Buhari yace kokarin gwamnatin yanzu shine maida hankali wajen neman hanyar samar da wuta dake amfani da rana domin magance matsalar fasa bututu da wadanda suke zaune a inda ake samar da iskar gas suke yi, da kuma gudun fuskantar karancinshi.
Dangane kuma da inganta harkokin noma, shugaba Buhari yace a shekarar dubu biyu da goma sha shida ya gayyaci ministan harkokin noma da kuma shugaban babban bankin duniya yace su nemi hanyar da zasu bi ta bada bashi ga manoma cikin sauki domin tallafawa masu karamin karfi ba tare da bin hanyoyin da aka saba bi ba, dake da tsawo kuma da wahalarwa ga kananan manoma. Banda haka kuma yace an samar da takin zamani isasshe wanda ya taimaki manoman da suka amsa kira suka rungumi noma, abinda ya taimaka wajen bunkasa harkokin noma.
Shugaba Buhari ya kuma ce rufe kan iyakoki da gwamnati tayi da hana shigo da shinkafa ya taimaka wajen samar da shinkafa ta cikin gida, duk da yake har yanzu ana fuskantar tsadar kayan masarufi. Shugaba Buhari yace tilas ne a yi maganin ‘yan sumogal idan ana so amfanin gona na cikin gida ya wadata, kuma a sayi abinda ake nomawa a cikin gida. Dalili ke nan da ya sa ya umarci hukumomi kada su bada rance ga wanda yake neman shigo da shinkafa.
A nashi bayanin, dan takarar shugan kasa na jam’iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, banda samar da wutar lantarki ta iskar gas, zai nemi hanyar samar da makashi da amfani da ruwa da zafin rana. Yace duk da yake babu teku a wadansu sassan Najeriya za a iya amfani da iskar gas wajen samar da wuta. Yace babu dalilin da yasa za a ce har yanzu babu isasshiyar wutar lantarki a Najeriya.
Alhaji Atiku Abubakar yace lokacin da yake matsayin mataimakin shugaban kasa, sun yi ayyuka da dama da suka hada da samar da hanyoyi wadanda da dama aka dakatar daga baya. Yace duk da yake ba shine shugaban kasa ba, ya iya neman a gudanar da wadansu ayyuka kuma an yi haka.
Dangane kuma da dangantaka tsakanin Najeriya da kasashen waje, dan takarar jam’iyar PDP yace Najeriya tafi kasashen Afrika da dama, sabili da haka Najeriya take matsayin da ake zuba mata ido a duniya, sai dai ya bayyana takaicin ganin Najeriya bata yin shugabancin da ya kamata sabili da gazawar shugabannni.
Dangane da batun hatsaniya da aka samu lokacin da shugaba Buhari ya je majalisa domin gabatar da kasafin kudin wannan shekara ta dubu biyu da goma sha tara, Alhaji Atiku yace, akwai bukatar samun kyakkyawar dangataka tsakanin dukan matakan shugabanci. Yace shugaba Buhari ya yi amfani da siyasa ya sami shugabanci amma shi ba dan siyasa bane, dalili ke nan ake samun sabani tsakaninshi da majalisa.
Saurari wannan bangaren hirar da Aliyu Mustapha ya yi da ‘yan takarar manyan jam’iyun siyasar Najeriya, Shugaba mai ci, Janar Muhammadu Buhari na jam’iyar APC, da kuma dan takarar babban jam’iyar hamayya PDP tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa.
Facebook Forum