Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Zaka Iya Raba Shafinka Na Facebook Da Duk Wani APP


Facebook
Facebook

Ko da mutum a yanzu ba ya amfani da wani APP a shafinsa na Facebook, tana yiwuwa ya taba amfani da wani APP din a can baya, kuma tana yiwuwa har yanzu wannan APP din yana nan makale a cikin manhajar Facebook ta mutum yana tattara bayanai game da kai ba tare da ka sani ba.

Idan kana son ka cire duk wani APP daga shafinka na Facebook, ba damuwa, akwai hanyar yin hakan.

Da farko kana bukatar bude shafinka Facebook a kan kwamfuta, sai ka duba a gefen hagu inda aka rubuta APPS, sai ka kai MOUSE, watau manuniyar kwamfuta jikin APPS zaka ga a gaba da shi Kalmar MORE, ko karin bayani ta fito. Sai ka matsa wannan kalma ta MORE.

Daga nan sai ka matsa inda aka rubuta SETTINGS a can saman shafin da ya bude, domin ya nuna maka dukkan jerin APPS dake cikin shafinka na Facebook.

Idan kana son kawar da duk wani APP da ka gani a cikin wannan jerin, kai manuniyar kwamfutarka ko MOUSE zuwa kan sunan wannan APP sai ka matsa aninin da zai fito da harafin X.

Daga nan zaka ga wani dan akwati ya fito yana tambayarka ko zaka cire wannan APP ne. Sai ka matsa inda aka rubuta Kalmar REMOVE, shike nan, ka yi ban kwana da wannan APP.

Da zarar ka cire wannan APP, to shafinka na Facebook zai daina tura masa duk wani sabon bayani na hoton da ka canja, ko abokin da kayi wa magana, ko wata ‘yar budurwar ko saurayin da aka yi chatting da ita ko hotunan da kuka yi musanya. Sai dai kuma, kada ka manta da cewa wannan APP yana dauke da bayanan da ya tattara daga shafinka kafin ka cire shi. Idan har kana son APP din ya goge wadannan bayanai n aka da ya tattara a can baya, to sai dai ka tuntubi kamfani ko mutumin da ya kera wannan APP din.

Jama’a, a yi hattara, a tabbatar cewa ana da bukatar wani APP sosai kafin a sanya shi a shafin Facebook. Kuma ko za a sanya, a rika nazarin irin bayanan da wannan APP ke tattarawa daga shafinka kafin ka sanya shi. Watakila in an fahimci irin sirrin mutum da APPS suke tattarawa, za a sake tunani kafin a sanya su.

A kashi nagaba, zamu fada muku yadda mutum zai iya sanya wani abu kan shafinsa na Facebook daga Twitter ko kuma sanya wani abu kan Twitter daga Facebook idan yana da su duka, ba tare da sai ya bude su duka a lokaci guda ya sanya ko ya rubuta abinda yake so din ba.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG