Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sata A Shagunan Mutane Na Haifar Da Koma Baya A Kasuwanci


Sata
Sata

A wani rahoto da wani kamfani a kasar Amurka mai suna “The Global Retail Theft Barometer” wato hukuma dake bincike akan masu sata a shagunan mutane, sun bayyanar da cewar a kowace shekara a kasar Amurka, masu shaguna su kanyi asarar kaya da kudin su yakai kimanin dallar Amurka billiyan gomasha uku $13, dai-dai da naira billiyan dubu biyu da milliyan dari takwas da sittin 2,860,000,000

Sua da yawa mutane kan je shaguna don siyayya, amma sai su kare da satar kaya a shagunan, wanda wasu ana samun damar kamasu, wasu kuwa sukan tsira. Mafi akasarin shaguna a nan sukan sa na’urorin kyamara da kuma wasu abubuwa da akan sasu a jikin kayan da ake siyarwa, wanda idan mutun zai fita daga shagon idan yana dauke da wani abu da yake bai biya kudin shiba, zaiyi kara a bakin kofa.

Haka kuma ma’aikata suma sukanyi sace-sace na abubuwa, suma masu kawon kaya daga kamfanoni kan sace wasu abubuwa, tun kamin isa shago. Duk dai wadannan dabi’un suna da hukunce-hukunce masu tsananin wahala. Hakan dai kansa mutun ya tafi gidan kasu idan aka kamashi, ko da kuwa abun da yata bashi da yawa ko tsada. Domin wannan yana nuna rashin tarbiyar mutun a fili.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG