Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Wata Kungiya Ke Tallafawa Matasa Su Zama Nagari


Wata kungiya da ke kula da yara masu tasowa – ‘yan shekaru 13 zuwa 19, ta kirkiri wata dabara ta nutsar da matasa ta hanyar kai su ziyara gidajen marayu, gidan kaso da gidan yara kangararru, da zimmar cusa masu ra’ayin zama ‘ya’ya na gari.

Kungiyar "Things development initiatives" mai zaman kanta, wacce kuma babu ruwanta da riba mai hedkwata a jihar Kano a Najeriya, ta himmatu ne wajen ganin an wayar da kan matasa domin ganin sun kaucewa fadawa harkoki shaye-shayen kwayoyi ko harkar daba.

“Yawanci za mu nuna masu ne cewa, idan kuka gujewa kullum abin da ake tsoratar da ku cewa kar ku yi, ba za ku fada cikin yanayin da wannan suka fad aba.” A cewar shugabar kungiyar Fadila Nuruddeen Muhammad a hirar da suka yi da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.

A cewar Fadila, wacce ta kammala digirinta a fannin aikin jarida, sukan kuma kai wa wadannan yara musamman ma wadanda suke gidan kaso "Pad" wato "Kunzugu" domin tsabtace jikinsu.

Amma ta lura cewa, idan suka kai musu a wannan karo, gobe wa zai ba su? Hakan ya sa ta yi bincike inda ta gano cewa wasu kasashen tuni suka daina amfani da Kunzugu na zamani.

Saboda haka Fadila ta kirkiri Kunzugu na zamani, ta hanyar amfani da auduga mai laushi, wacce aka sarrafa ta tamkar kunguzun zamani, aka nade ta da zani, akan kuma wanke da zarar an gama amfani da ita.

Fadila har ila yau tana karantu a fannin “Special Education” wato bangaren masu bukata ta musamman.

“Yawanci ina ganin kamar al’umarmu ba ta ba su irin gudunmuwar da ta kamata, ba ma a lura da cewa suna da bukata.” In ji Fadila.

Ta kara da cewa da zarar ta kammala wannan karatu na ta, za ta fito da wata hanya mafi sauki da za’a dama da masu bukata ta musamman a harkokin yau da kullum.

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:56 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG