Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Yi Jana’izar Fasto T.B Joshua


Marigayi TB Joshua (Instagram/tbjoshua)
Marigayi TB Joshua (Instagram/tbjoshua)

A karshen makon nan aka gudanar da jana'izar karshe ta babban malamin addinin Kirista Pastor Temitope Balogun Joshua, wanda aka fi sani da T.B. Joshua.

An gudanar da jana’izar ne a cocinsa ta Synagogue of All Nation da ke jihar Legas a kudu maso yammacin Najeriya.

Rahotanni sun ce an binne shi da misalin karfe 2:50 a gaban iyalansa da wasu baki na musamman da aka gayyata.

Da yawa daga cikin mabiyansa da suka halarci jana’izar sun kalli hidindimun binne shi ne ta kafar talabijin da aka saka a cikin zauren cocin.

Jana’izar, wacce aka yi a ranar Juma’a ita ce mataki na karshe da aka yi a jerin shirye-shriyen binne fitaccen malamin addinin Kiristan, wanda aka kwashe mako guda ana yi.

Dubban mutane ne suka hallara a wajen binne malamin daga sassan duniya.

Wani abu da ya sa TB Joshua yin fice a duniya shi ne, ikirarin da ya yi, na cewa yana iya warkar da cututtuka iri-iri, ciki har da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDS.

Hakan ya sa jama’a daga sassan duniya, kan yi tattaki har zuwa Najeriya don neman waraka.

Kazalika, kamar yadda rahotanni ke nunawa, TB Joshua, malami ne dake ikirarin iya hangen abin da zai faru a gaba, lamarin da ya jima yana janyo ka-ce-na-ce.

Katafaren ginin Mujami'arsa da ke Legas ya taba ruftawa a shekarar 2014, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 100 ciki har da ‘yan kasar Afirka Kudu da dama.

A ranar 5 ga watan Yuni T.B. Joshua ya rasu, yana da shekara 57.

XS
SM
MD
LG