A wani sabon yunkuri na ta da komadar tattalin arzikin wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, musamman a arewa maso gabashin Najeriya, hukumomin kai dauki ga mazauna yankin da lamarin ya fi shafa.
Hukumomi da kuma kungiyoyi masu zaman kansu sun kirkiro dabaru na koyawa magidanta da kuma mata hanyoyin kiwon zamani domin su rike kansu.
Shirin ya gudana ne karkashin kwamitin tallafawa al’ummomin arewa maso gabas wato, Presidential Committee on North East Initiative (PCNI) na gwamnatin tarayya.
Ya kuma hada har da hadin gwiwar cibiyar bunkasa harkokin ci gaba ta Centre for Social Change and Economic Development (CSCED.)
A lokacin taron, an ba da tallafin awaki ga magidanta da mata 550, a yankin Mubi, daya daga cikin yankunan da suka yi fama da rikicin Boko Haram a Jihar Adamawa.
Kwamishinan ma’aikatar harkokin dabbobi na jihar Adamawa, Alhaji Usman Yahaya, ya yaba da alfanun wannan tallafi na awaki da kayakin aikin ga al’ummomin karkara.
Ya kuma yi fatan za’a ci gaba da samun irin wannan hadaka domin tallafawa masu karamin karfi.
Wakilan hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO), Mr. Usman Palam, da hukumar ba da agajin gaggawa a Najeriya (NEMA), Mr Yusuf Ibbi, da kuma hukumar kai dauki a JiharAdamawa (ADSEMA), Malam Mohammed Buba, sun yaba da wannan mataki.
Saurari cikakken rahoton Wakilin Muryar Amurka, Ibrahim Abdul'aziz.
Facebook Forum