Hamisu Sodangi wanda aka fi sani da "Raven", mawaki ne na hip hop wanda ya ce sha’awa ce ta ja shi ga harkar waka, kuma a mafi yawan lokutan yana isar da sakonnin da suka shafi yawan shaye-shayen kwayoyi da ke adabar matasa a yanzu.
Ya ce ya fara waka ne sanadiyar yawaitan sauraron wakokin mawakan waje, sannan abin da ya sa ya fara waka domin isar da sakonnin biyayya ga matasa domin su zama masu tarbiya, da zama matasa na gari tare da kauracewa shan kwayoyin da ake yi a yanzu.
Ya bayyana cewa lokaci yayi da matasa zasu san cewar yawan shaye shayen kwayoyi baya haifar da da mai ido, wato ba wani abu ne mai kyau ba, illa kai matashi ga halaka da rashin samun rayuwa mai inganci.
Daga cikin kalubalen da mawaka kamar Raven ke fuskanta sun hadar da rashin bada hadin kai daga wajen iyaye a lokacin da mawaka irinsa ke fara waka, amma daga baya ya ce ya samu goyon bayan da ya dace.
Har ila yau ya ce suna fuskantar matsaloli da rashin hadin kai daga wajen mawaka da basa tallafawa junansu domin cimma muradan da suka sanya a gaba.
Ya kara da cewa akwai matsala ta rashin zuba hannun jari daga alummar gari da ma gwamnati ita kanta domin talafawa matasan da su ka zabi waka a matsayin sana'arsu.
Facebook Forum