Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Za ta Fara Kwashe 'Yan Kasarta Daga Kasashen Ketare


Kasar Ghana kamar wasu kasashen duniya ta saurari kiran da ‘yan’yanta da suka makale a wasu kasashe sakamakon matakan hana zirga-zirga da kasashen duniya suka dauka domin dakile annobar coroanvirus da ta ddabi duniya.

A makon da ya gabata ne ma’aikatar harkokin wajen Ghana ta fitar da wata sanarwa a kan shirye-shiryen da gwamnati ke yi na dawo da ‘yan kasar da suka makale a kasashe da dama.

Shugaban sashen hulda da jama’a da yada labarai na ofishin jakadancin Ghana a Amurka Kofi Tonto, ya ce ofinshinsa ya sami umarni daga ma’aikatar harkokin wajen Ghana cewa ya tattara sunayen ‘yan kasar da wadanda suke da izinin zama kasar da suka makale a Amurka domin a dawo dasu gida.

An tambayi Kofi Tonto ko akwai yiwuwar gwamnati zata kwashe dukkan ‘yan Ghana mazauna Amurka, inda ya ce, “hakan ba zai yiwuwa ba har sai shugaban kasa ya dauki matakan da suka dace domin ba da izinin yin haka, inda za a yi marhabin da duk wani dan kasa ko da mazaunin Amurka ne, ko ma ya zama ba-Amurke, amma dai yanzu ana maganar ‘yan Ghana ne da suka je wata harka suka makale.

Mutanen da za a maida su gida daga yankin jihohin New York, New Jersey da Connecticut za su kai sunayensu ne a karamin ofishin jakadancin Ghana dake New York, kana wadanda suke a sauran jihohin Amurka za su gabatar da sunayensu ne ga babban ofishin jakadancin Ghana dake Washington DC. Ya kuma ce tuni suka tattara sunayen sama da mutane 500.

Kofi Tonto ya yi wa ma’aikacin muryar Amurka bayani akan ko gwamnati ce za ta biya kudin jirgin mutanen, inda ya ce, “a dadai wannan lokaci mutanen ne za su biya kudin jirginsu har sai an gama tattara bayanan matafiyar saboda a cikin takardun da suke cikewa akwai tambayar da aka yi musu ko za su iya biyan kudin jirgi ko a’a, dan haka sai bayan an kamala tattara su za a tabbatar da ko gwamnati za ta daukin nauyin kudin jirgin ko kuma za ta rage musu wani abu.

Mohammed Mada tsohon shugaban kungiyar ‘yan Ghana kuma babban jami’i a hadaddiyar kungiyar ‘yan Afrika a New York ya ce, duk da cewar ba Amurka kadai gwamnatin za ta kwashi ‘yan Ghanan ba, taimakawa da kudin jirgi ba illa ba ne indai tana iya yin hakan.

Ofishin jakadancin Ghana a Amurka ya ce, nan da mako mai zuwa za a fara jigilar mutanen zuwa Ghana.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Baba Yakubu Makeri.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG