Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya jaddada cewa dole ne a kammala yarjejeniyar sako mutane kusan 100 Da Hamas ta yi garkuwa da su kafin rantsar da shi kasa da mako biyu masu zuwa.
Trump ya sake jaddada barazanarsa cewa Gabas ta Tsakiya za ta shiga tsaka mai wuya idan ba a sako wadanda aka yi garkuwa da su ba kafin bikin rantsar da shi a ranar 20 ga watan Janairu.
Trump yace, ‘Ba na so in yi katsalandan a tattaunawar batun yarjejeniyar amma idan wadanda aka yi garkuwa da su ba su dawo gida ba kafin na kama aiki, to Gabas ta Tsakiya za ta shiga tsaka mai wuya, ba za ta yi wa Hamas dadi ba, maganar gaskiya shi ne, ba za ta yi wa kowa da kowa dadi ba, Ba sai na kara maimaitawa ba. ya kamata a ce tuntuni an sako wadanda a ka yi garkuwa da su baki daya. Bai kamata a yi garkuwa da su ba tun farko. Bai kamata a kai harin ranar 7 ga Oktoba ba."
Wakilin Trump na musamman a Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff, wanda shi ma ya yi jawabi a takaice a wani taron manema labarai a Mar-a-Lago gidan Trump, ya ce yana sa ran kai ziyara Qatar a ranar Talata ko Laraba amma bai bayyana wanda zai gana da su ba a ziyarar tasa a yankin.
Dandalin Mu Tattauna