Tsohon direban bas na daukar ‘yan makaranta Ariel Castro, wanda aka gani da sabon gemu fari, ya bayyana gaban wata kotu jiya jumma’a a birnin Cleveland cikin kayan fursunoni mai launin lemo. A lokacin ya amsa aikata laifuffuka guda 937 da ake tuhumarsa a kansu, ciki har da daruruwa da suka shafi sace wadannan mata, da daure su da sarka tare da yi musu fyade har sai bayan da daya ta samu kubucewa a cikin watan Mayu kafin ‘yan sanda su kwanto saura biyun.
Castro, mai shekaru 53 da haihuwa, ya kuma amsa laifin kisan kai a wannan lamarin ta hanyar yi ma daya daga cikin matan ciki, sannan ya lakkada mata mummunar duka har sai da ta yi bari. Daya daga cikin matan kuma ta samu cikin yarinya a lokacin da take daure a gidan Castro har ta haifi yarinyar da yanzu shekarunta 6.
Babu daya daga cikin matan su uku wadanda Castro ya sace daga kan titi daga shekarar 2002 zuwa 2004, da ta bayyana a cikin kotun. Kwanakin baya suka yi wani faifan bidiyo su na godewa mutanen birnin Cleveland a saboda goyon bayan da suka ba su a lokacin da suke daure.
Alkalin yace za a bayyana hukumci kan Castro a shari’ance a cikin mako mai zuwa.