To sai dai a ganin Dr. Usman wannan ziyara ta Obama ta fi ta kowane shugaban Amurka, domin babu wanda ya zagaya kamar yadda Obama ya yi. A karo na farko Obama ya je Ghana. Sai gashi a karo na biyu ya zagaya kasashe da dama.
Dr. Usman ya ce yawanci idan shugaban Amurka ya yi tafiya ya kan je da babbar jaka ta yabama yadda kasashe suka yi zabe inda 'yan hamayya suka ci kuma aka mika masu mulki ba tare da wata matsala ba. Wannan wata hanya ce ta karfafa dimokradiyya.
Sai dai kamar yadda ya ce za'a iya yaba ma shugaban amma kwalliya bata biya kudin sabulu ba, dalili kuwa shi ne yadda Obama ya so ya cusa ma shugaban Senegal ra'ayin aure tsakanin jinsi daya. Shi kuma shugaban Senegal nan take ya ce sai dai Amurka. A nan an samu matsala domin dama kudirorin Amurka Obama yake so ya sayar lamarin da ba zai yiwu ba.
Sanin cewa mahaifin Obama dan asalin Afirika ne Aliyu Mustaphan Sokoto ya tambayi Dr Usman ko yayi mamakin yadda Obama ya yi kokarin cusa ra'ayin aure tsakanin jinsi daya?
Dr. Usman ya amsa yana cewa shi bai yi mamaki ba domin irin akidar da ya tashi da ita kenan koda yake shi kanshi bai yarda da ita ba amma akida ce na barin kowa ya yi abun da yake so yadda 'yanci ya bashi.
Ya ce kuma abun gagarumin mamaki ne domin ya zo lokacin da kotun kolin Amurka ya yanke hukuncin cewa aure ba wai sai namuji da maje ba. A'a kowa na iya auren wanda ya ke so kodama jinsi daya ne.
To amma a Afirka maganar auren jinsi daya ma bata taso ba domin majalisu da yawa sun yi watsi da maganar. A kasashe kamar Najeriya an yi dokar da ta hana wannan aure kacokan. Dr. Usman ya yi mamakin yadda Obama yayi kokarin cusa wannan ra'ayi maimakon ya maida shi kamar ba wani abu ba ne. A Amurka akidar ce ta sa ya ci zabe domin ya yi wa 'yan lu'adi da 'yan madigo cewa zai samarmasu 'yancin yin aure. Lamarin kuma ya tabbata.
Sai dai ya ce dole ne a yaba masa da ziyarar da ya kawo Afirika domin babu wani shugaban Amurka da ya taba zagayawa kamar yadda ya yi.
Akwai karin bayani.