Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wike Ya Sallami Shugabannin Ma'aikatun Birnin Abuja 21


Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Ezenwo Wike
Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Ezenwo Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya amince da sallamar shugabannin ma’aikatu da kamfanonin gwamnati 21 da ke karkashin birnin na Abuja.

Daraktan yada labarai na ofishin Ministan, Anthony Ogunleye ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Ga wasu daga cikin hukumomi, ma'aikatu da kamfanonin da lamarin ya shafa:

- Hukumar saka hannayen jari ta Abuja

- Hukumar kula da kasuwannin Abuja

– Babban shugaban MD/CEO, Kamfanin Sufuri na Abuja

- Shugaban(MD), Kamfanin Raya Kadarorin Abuja

- Hukumar yada labaran birnin Abuja

- Hukumar samar da ruwa ta Abuja

- Hukumar ba da agajin gaggawa ta Abuja

- Ma’aikatar lafiya amatakin farko ta Abuja

- Hukumar kula da asibitocin Abuja

- Hukumar kare muhalli ta Abuja

- Hukumr ba da tallafin karatu ta Abuja

- Hukumar jin dadin Kiristoci masu zuwa Ziyarar Ibada

- Hukumar Alhazai ta Abuja

- Hukumar inshorar lafiya ta Abuja

- Hukumar raya garuruwan kewayen Abuja

- Hukumar kula da tsakiyar birnin Abuja

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Ministan ya umarci shugabannin hukumomin da su mika dukkan al’amuran ofisoshinsu ga manyan jami’an ofishin da ke biye da su a girman mukami.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG