Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

WHO Ta Yi Kira Ga Kasashen Afirka Su Dauki Kwararan Matakai Kan COVID-19


Darektar WHO a nahiyar Africa Matshidiso Moeti
Darektar WHO a nahiyar Africa Matshidiso Moeti

Hukumar lafiya ta WHO ta yi kira ga kasashen nahiyar Afirka, da su dauki kwararan matakai don dakile yaduwar cutar COVID-19, yayin da kasashen yankin suka fara maido da harkokin sufurin jiragen sama.

Tattalin arzikin nahiyar wanda wani kasonsa ya dogara akan harkar sufurin jirgagen sama da yawon bude ido, ya fuskanci tawaya sanadiyyar annobar coronavirus da duniya ke fuskanta.

A jiya Alhamis Darektar Hukumar ta WHO a nahiyar Afirka Dr. Matshidiso Moeti ta fada cikin wata sanarwa cewa, “fannin sufurin jiragen sama na taka muhimmiyar rawa ga tattalin arzikin kasashe, “amma yayin da muka maido da zirga zirgar jiragen, akwai bukatar mu ci gaba da kiyaye matakan da aka saka na kare yaduwar cutar.”

A lokacin da annobar ta yi kamari, kasashe 36 da ke kudu da Saharar Hamada sun dakatar da zirga-zirgar jiragen sama, inda har takwas daga cikinsu suka hana jiragen da suka fito daga kasashen da cutar ta yi tsanani shiga yankunansu.

A halin da ake ciki Kamaru, Equatorial Guinea, Tanzania da Zambia sun maido da sufurin jiragen yayin da kasashe 15 daga yankin yammacin Afirka suke shirin bude iyakokinu a ranar 25 ga watan Yuli.

Wannan sanarwa da hukumar ta fitar na zuwa ne, bayan da Kwamishinan ayyuka da makamashi a kungiyar tarayyar Afirka, Amani Abou-Zeid, ya ce nahiyar ta tafka asarar dala biliyan 55 a fannin tafiye-tafiye da yawon bude ido, cikin wata ukun da suka gabata sanadiyyar cutar ta coronavirus.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG