A hari guda, wasu ‘yan bindigar da suka yi shiga irinta sojoji, sun kai farmaki a kan garin Konduga ranar lahadi da asuba, suka bude wuta kan mutanen dake yin sallar asuba a cikin wani masallaci. Haka kuma, sun cunna wuta a gidajen dake kusa da nan. ‘Yan sanda suka ce an kasha mutane 47, aka ji rauni ma wasu 39. Sannan an kona gidaje guda hamsin.
Hakimin Konduga, Zannah Musa Yale, yace wasu daga cikin wadannan mahara mata ne. Gwamna Shettima Kashim na Jihar Borno ya ziyarci garin na Konduga jiya talatya ya kuma yi alkawarin biyan diyya ga iyalan da abin ya shafa.
A wani harin dabam, ‘yan bindigar sun shiga kauyen Ngom suka kasha mutane 12 daren asabar.
Babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai wannan harin, amma jami’ai sun a kyautata zaton kungiyar nan ce ta Boko Haram ta kai. A baya, kungiuyar Boko Haram ta dauki alhakin kai hare-haren da suka hada har da kan masallatan da limamansu suka yi tur da tsagerancin addini.