Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Sabuwar Mahaukaciyar Guguwa Mai Suna Nate Na Barazana Ga Sashin Amurka


Mahaukaciyar guguwar Nate
Mahaukaciyar guguwar Nate

Ana wata, ga wata. Tun Amurka ba ta gama murmurewa daga bala'o'in guguwan da su ka gabata ba, sai ga wata kuma mai suna Nate ta bullo.

Mahaukaciyar guguwar nan ta Nate ta dira kusa da kogin Mississipi, kuma ana kyautata zaton za ta dira karo na biyu a kusa da bakin gabar Mississipin cikin 'yan sa'o'i masu zuwa, kuma ana ganin lawalinta ya game fadin jahar, kuma daga bisani zai ma hada da jahohin Alabama da Tennessee zuwa daren yau Lahadi agogon yankin.

Cibiyar Nazarin Mahaukaciyar Guguwa ta ce iskar da guguwar ta Nate ke kadowa ta rage gudu zuwa kimanin kilomita 85 a sa'a guda, ana kyautata zaton karfin guguwar zai dada raguwa yayin da ta cigaba da tafiya bisa doron kasa, ta yadda za ta ragu ta zama guguwar yankin tropic zuwa yammacin yau Lahadi.

Jami'an yankin na kira ga mazauna yankin da su kasance cikin gida har sai guguwar ta wuce. Magajin Garin New Orleans Mitch Landrieu ya gaya ma al'ummarsa da ma 'yan yawon bude ido da ke kai ziyara a New Orleans din cewa su yi kaffa-kaffa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG